Usman Bayero Nafada

Usman Bayero Nafada (An haife shi ne a watan Janairu, shekara ta alif 1961) anhaifeshi a ƙaramar hukumar Nafada dake garin Gombe.tsohon mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai ne a Najeriya kuma ɗan jam'iyyar PDP mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Dukku/Nafada na jihar Gombe. Shi ne ɗan takarar gwamna a zaɓen gwamna na shekarar 2019 a jihar Gombe. An haifi Usman Bayero Nafada a watan Janairun shekarar 1961 a cikin jihar Gombe. Yana da takardar shedar malanta daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), dake Zariya, Jihar Kaduna. Yana kuma da digiri a lissafi daga Jami’ar Maiduguri, dake a Maiduguri, Jihar Borno. Nafada memba ne a majalisar wakilai ta Gombe ga jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) daga shekarar 1999 har zuwa shekarar 2003, kuma ya riƙe muƙamin kakakin majalisar a lokacin. An zabi Nafada ne a majalisar wakilai ta kasa a shekara ta 2003 a matsayin dan takarar ANPP daga Dukku / Nafada, amma ya sauya sheka ya zama memba na PDP lokacin da jiharsa ta fara jefa kuri'ar hakan. Bayan murabus din Babangida Nguroje a tsakanin cin hancin da rashawa na shugabar majalisar Patricia Etteh. A watan Yuli na shekarar 2018, kasa da shekara daya da zabe, Sanata Nafada, tare da wasu mambobi 14 da suka fice daga jam'iyyar APC zuwa PDP. Nafada yayi takarar gwamnan Gombe a shekarar 2019


Developed by StudentB